Ma’anar wala’i da bara’a ko kuma ji...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar wala’i da bara’a ko kuma jibinta da kiyayya

Tambaya

Mene ne ma’anar wala’i da bara’a, ko kuma jibinta da kiyayya, ta yaya kungoyoyin ‘yan ta’adda suka yi amfani da wannan ma’anar wurin yada ta’addanci?

Amsa

Idan muka yi duba zuwa ga litattafan magabata cikin managartan mutane na da, da na yanzu, ba za mu samu wani gurbi mai dauke da ma’anar wala’a da bara’a ba, sai dai cewa wannan ma’ana ne sabuwa wadda wasu sashen mutane suka kirkiro, ma’anarsa yana juyawa ne akan soyayya da kiyayya saboda Allah, sun raya cewa wai hakan da asali ko dalili a Alkur’ani da Sunna. Daga ciki akwai inda Allah yake cewa: (Kana ganin mafi yawa daga cikinsu suna jibintan wadanda suka kafirce kaicon abin da kawukansa ke gabatarwa, to Allah ya yi fushi da su) [Al-ma’ida: 80], shi “Jibinta” yana nufin soyayya da kusanci, akasin tuburewa wanda yake nufin kiyayya da adawa, haka nan masu tsattsauran ra’ayi sun yalwata hanyoyin amfani da wannan musdalah din har sai da suka cusa shi cikin akida, a cikin ma’anar “la ilaHa illallaHu” sai suka kirkiro da abin da ake kira da Al’wala’a da Al’bara’a, cewa ita sharadi ne na imani, suka ce lallai rashin tabbatar da wannan akidar zai shigar da mutum cikin kafirci bisa dalilin fadin Allah Madaukakin Sarki: (Wanda ya jibince su daga cikinku, to lallai yana cikinsu) [Al’ma’ida: 51], sai aka wayi gari misali son wani mutum na kowa wanda ba Musulmi ba ko kuma Musulmi, sai dai duk abin da bai dace da tunaninsu ba, to kafirce wa Allah Madaukakin Sarki ne!.

Share this:

Related Fatwas