Ma’anar Daula a Musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar Daula a Musulunci

Tambaya

Menene ma’anar  Daula a Musulunci, kuma ta yaya kungiyoyin ‘yan ta’adda suka bar wannan ma’anar suka sauya shi da ma’anar kungiyanci?

Amsa

Duk wata Daula a Musulunci tana kasantuwa ne daga ginshikai guda uku, ginshiki na farko shi ne, “kasa” wato taswiran  wuri da ake zaune a cikinsa. Abu na Biyu kuma shi ne samuwar “mutane” wato al’ummar da suke zaune a wancan wurin da aka ambata a baya, wasu malaman fikihu sun shardanta cewa dole ne mafiya yawan mazauna wannan wuri su kasance Musulmai ne, Abu uku kuwa shi ne “Tsari” wato tsarin dokoki ma’abota tushe da suke tsara dangantaka tsakanin mai mulki da wanda ake mulka, hakan tsakanin wadanda ake mulka a tsakaninsu, haka nan tsakanin wannan kasa da wasu kasashen na daban. To a irin haka ake samar da daula ta Musulunci wacce aka gina ta bisa tsarin hukunci na Musulunci, wannan shi aka fi sani da mabubbuga shari’a a cikin kundin tsarin mulki.

Amma fa su kungiyoyin ‘yan ta’adda wasu mutane ne da suke da wasu tsare - tsare nasu na siyasa da suke fada ko rikici da duk wadanda suke kusa da su, domin suna adawa da kasashen Turawa da na Larabawa da na Musulmai, haka nan suna adawa ta tsarin da yake tafiyar da wadancan kasashen da shugabanninsu da kuma al’ummunsu, kai lamarin ma yana kai wa ga su yi fada da junansu, “fadan cikin gida” saboda su tunaninsu ya rataye ne da duk abin da ke da dangantaka da tsauri ko zafafawa, sannan kuma su yi ikirarin cewa wai suna kan manhajin Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da sauran magabata na kwarai, to irin halayyar wadannan mutanen yana daidai da lamarin cutar kansa a cikin jikin mutum.

Share this:

Related Fatwas