Ambaton Allah a kowane yanayi
Tambaya
Shin ya halatta mai janaba ya yi zikiri da tasbihi?
Amsa
Zikiri shi ne ibadar da Allah Madaukaki ya yalwata mata lokaci da sharudda da yanayi, ana so a yi shi a kowane irin yanayi, a kuma kowane irin lokaci, a kuma cikin tsarki ko ba a cikin tsarki ba; umurnin yin zikiri ya zo ne ba tare da kaidi ba, wannan sai ya nuna halaccin yin zikiri a kowane hali mutum ya kasance a ciki; Allah Madaukaki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani, ku ambaci Allah sosai, ku kuma yi masa tasbihi safiya da maraice) [al- Ahzab: 41- 42], Allah Madaukaki ya ce: (Lallai a cikin halittar da Allah ya yi wa sammai da kasa, da abubuwan da suke cikin su na kwarewa da gwaninta, da sabanin da dare da rana suke da shi, na haske da duhu, tsawo da gajerta, akwai bayyanannun ayoyin ga masu hankalin da suke iya riskar kadaitakar Allah da ikon sa. Shi kuwa sha'anin masu hankali –a koda yaushe- shi ne su halarto da girman Allah da buwayan sa cikin zukatan su, a kuma duk inda suke, shin suna tsaye ne, ko a zaune, ko a kwance, suna tunani akan halittar sammai da kasa, da abubuwan da suke cikin su na ban mamaki, suna cewa: ya Ubangijin mu, lallai ba ka halicci wadannan abubuwa ba sai domin hikimar da ka hukunta, kai ka tsarkaka ga barin tawaya, a'a, ka halicce su ne domin su zamo dalilai da za su yi nuni akan ikon ka, su kuma zamo alamu ne da za su nuna isar hikimar ka; saboda haka, ya Ubangiji ka tsare mu ga barin azabar wuta, ta hanyar katartad da mu zuwa ga hanyar yi maka biyayya..) [Ali Imran: 190- 191].
Lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana yin zikirin Allah Madaukaki a dukan lokutansa, da duk yanayin da yake ciki (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); an ruwaito Hadisi daga Sayyida A’isha ummul muminina (Allah ya kara yarda da ita) ta ce: (Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana ambaton Allah a duk yanayin da yake ciki) [Muslim].
Imam al- Nawawiy ya nakalto ijma’in malamai akan halaccin zikiri a zuci da harshe, ga wanda ba shi da alwalla da mai janaba, da mai al’ada da mai biki; a cikin littafinsa “al- Azkar” (shafi na 11) ya ce: “Malamai sun yi ijma’i akan halaccin yin zikiri da zuci da harshe ga wanda ba shi da alwalla, da mai janaba, da mai al’ada da mai biki, wajen yin tasbihi da tahlili da tahmidi da takbiri da yi wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati da addu’a da sauransu”.
Allah shi ne masani.