Lokacin sallar walha da yawan raka'...

Egypt's Dar Al-Ifta

Lokacin sallar walha da yawan raka'o'inta

Tambaya

Wane lokaci ne ake yin sallar walha? Kuma raka'a nawa ne da ita?

Amsa

Lokacin walha yana farawa ne tun daga bayan dagawar rana zuwa kafin lokacin zawali (ma'ana bayan fitowar rana da kaman minti ashirin zuwa kusa da sallar azuhu da kaman minti hudu), mafi karancin raka'o'inta kuwa su ne raka'a biyu, amma an fi so a yi raka'a hudu zuwa sama; lallai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana sallar walha raka'a hudu, yana kuma yin sama da haka yanda yake so.

Share this:

Related Fatwas