Ambaton Allah yayin cin abinci.

Egypt's Dar Al-Ifta

Ambaton Allah yayin cin abinci.

Tambaya

Mene ne hukuncin ambaton Allah a farkon cin abinci? Mene ne hukuncin wanda ya manta sannan ya tuna lokacin yana tsakiyar cin abinci.

Amsa

Shi ambaton Allah a yayin cin abinci sunnah ne, saboda hadisin Umar bin Abi Salama Allah ya kara musu yarda ya ce: Na ci abinci tare da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sai hannuna ya fara rawa da na sanya cikin akushin, sai Manzon Allah ya ce: (Ka ambaci sunan Allah, sannan ka ci da hannunka na dama, kuma ka ci abin da yake gabanka). Abu Dauda.

Duk wanda ya manta ambaton Allah a farkon cin abincinsa to ya ambata a duk sanda ya tuna, sai ya ce: “BismillaHi Auwaluhu wa Akhiruhu” saboda hadisin Sayyidah Aisha Uwar muminai Allah ya kara mata  yarda tace: Lallai Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa sallam ya ce: Idan dayanku zai ci abinci to ya ambaci sunan Allah, idan ya manta ambatonsa a farko to ya ce: “BismillaHi Auwaluhu wa Akhiruhu” Abu Dauda.

Allah Madaukakin Sarki ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas