Sujadar tilawar Alkur’ani

Egypt's Dar Al-Ifta

Sujadar tilawar Alkur’ani

Tambaya

Me ake karantawa a lokacin da ake karanta, ko aka ji ana karanta ayar sujadar tilawar Alkur’ani mai girma a cikin yanayin da mutum ba shi da ikon da zai yi sujadar nan take?

Amsa

An so idan Musulmi ya ji, ko ya karanta ayar sujada a yanayin da ba shi da ikon yin sujadar ya karanta wasu zikirori da addu’o’i.

Sujadar tilawar Alkur’ani sunna ce mai karfi, saboda maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Idan mutum ya karanta ayar sujada, sannan ya yi sujadar, shaidan zai nesance shi, yana kuka, yana cewa: kaico na!) [Muslim]. Kafin sujadar tilawa ta zama ingantacciya an shardanta yin tsarki, ma’ana ya zama mutum yana da alwalla, da tsarkin jiki da na tufafi da na wuri, ya kuma fuskanci alkibla, da suturta al’aura, ba daidai ba ne a yi sujadar tilawa idan ba a cika wadannan sharudda ba, idan mutum bai cika wadannan sharudda ba, ko ba shi da ikon da zai iya yin sujadar, sai ya karanta: “SubhanalLahi, walhamdulilLahi, wa la’ilaha illalLahu, walLahu akbar, walahaula walakuwwata illabilLahil Azim” sau hudu, ko ya kawo wani zikiri da addu’a ire- iren wannan wadanda suke kunshe da yabo da jinjina ga Allah mai girma da buwaya.

Share this:

Related Fatwas