Taimakekeniya kan da’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Taimakekeniya kan da’a

Tambaya

Mene ne ladar da ake samu a wurin aikin sa kai ta hanyar kwarfe ruwan da ya taru a kan hanyoyi?

Amsa

Taimakekeniya ta fuskar yin abu nagari tare da kwararru a sashen wurin taimaka musu kan kwashe ruwan saman da ya malala a kan hanyoyi domin karkatar da ruwan zuwa ga magudana, to wannan abu ne mai samarwa mutum lada daga Allah Ta’ala, share hanyoyi da tituna daga ruwan da ya taru sakamakon ruwan sama tare da kora ruwan zuwa magudanun da aka ware na musamman abu ne da ake bukata, kamar yanda mutum zai samu lada mai yawa sakamakon hakan a wurin Allah Ta’ala, kawar da kazanta daga kan hanya yanki ne daga cikin yankunan imani, hakika malamai sun yi bayani kan cewa abin da ake nufi da kawar da kazanta daga kan hanya shi ne : Duk wani abu da zai iya cutar da mutane kama daga dutse, ko ruwan sama, ko tabo, ko kaya, ko duk wani abu da ke iya cutar da mutane, hakanan sare bishiyoyi daga wuraren da ke baiwa mutane tsoro, duk irin wadannan ayyukan ana son aikatawa, daga cikin irin wadannan kyawawan ayyukan akwai cike rijiya da ta fado kan tsakiyar hanya wacce ake tsoron kar makaho ko yaro ko dabba su iya fadawa ciki, ya wajaba a cike ta, ko kuma a kewayeta da makari matukar hakan ba zai cutar da masu wucewa ba.

Share this:

Related Fatwas