Yin wa’azi lokacin birne mamaci

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin wa’azi lokacin birne mamaci

Tambaya

Shin ya halasta ayi wa’azi a lokacin da ake birni mamaci?

Amsa

Babu laifi ayi wa’azi a takaice da zai tunatar da mutane mutuwa da lahira a yayin rufe mamaci. An karbo daga Amirul Muminina Aliyu Karramal Lahu wajhahu ya ce: (Mun kasance a wurin wata jana’iza a makabatran bakiyar Garkad, sai Annabi S.A.W. yazo mana sai ya zauna, mu ma sai muka zauna a gefensa, tare da shi akwai sanda, sai  ya sunkuyar da kansa kasa yana nazari tare da jinjina sandarsa, sanna ya ce: Babu wani a cikinku, kuma babu wata rai da ake busa mata numfashi face anyi mata masauki a Aljanah ko kuma a Wuta, don in ba haka ba ai an riga an rubatawa ran makoma domin kasancewa tababbiya ce ko wadatacciya). Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, Shin ba zamu dogara kawai da abin da aka rubuta mana ba? Sai Manzon Allah ya ce: (Kuyi aiki, kowa abin saukakewa aikin da aka samar dominsa ne) Anyi ittifaki akan Hadisin.

Share this:

Related Fatwas