Ma’anar hijira a Addinin musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar hijira a Addinin musulunci

Tambaya

Mene ne mahangar addini a yanzu bisa fahimtar hijira? Shin ya wajaba ga wanda yake rayuwa a kasashen da ba na musulmai ba da ya kaurace musu domin tsira da addininsa zuwa wani gari na daban kamar yanda masu tsattsauran ra’ayi ke yawan nanatawa?

Amsa

Kungoyoyin masu tsattsauran ra’ayi da na ‘yan ta’adda sun gauraya ma’anar hijira a fuskar gama garin mutane, inda suka wajabtawa duk wani da yake rayuwa a kasashen da ba na musulmai ba da ya gaggauta barin kasar zuwa wata kasa ta daban ta musulmai, sakamakon hakan shine tsira da addininsu da kiyaye akidarsu, don haka duk wannan yana karkashin ma’anar hijira ta shari’a a musulunci kamar yanda suke rayawa.

A zahirin gaskiya hijira ita ce ilimin samin canza yanayin da ake ciki zuwa ga mafificin yanayi, domin samun al’umma cikakkiya mai hadin kai da juna, wata kila wannan ma’anar ne Annabi SallallHu AlaiHi wasallam yake nufi bayan bude Makkah inda ya ce : “Babu hijira  bayan bude Makkah, sai kawai jihadi da kuma niyya” Muslim.

Abin nufi anan shine bayan bude garin Makkah to babu wani abu da zai wajabta yin hijira zuwa garuruwa, kai bugu da kari ma akwai abin da ke farlanta kauracewa masa kamar munanan tunani zuwa ga kyawawa, yana daga cikin abinda lalacewarsa ya tabbata ko gurbatansa zuwa ga abinda muke zato ko muke gani a samu alheri da sauye sauye acikinsa.

An karbo daga Abdullahi bin Amru bin Aas Allah ya kara musu yarda, cewa Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wasallam ya ce : (Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, muhajiri kuma shine wanda ya kauracewa abinda Allah yayi hani akansa) Bukhari.

Share this:

Related Fatwas