Tarihin kafirta Musulmi a cikin al’...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tarihin kafirta Musulmi a cikin al’ummar Musulmai

Tambaya

Mene ne ya sanya kafirta Musulmai ya yadu, ya kuma fi yawaita a harsunan kungiyoyin ‘yan ta’adda?

Amsa

Tarihin jifan Musulmai da kalmar kafirci yana komawa ne zuwa ga bin manhajin Hawarijawa, wadanda a zahirinsu suke bayyana da sunan Musulunci, wadanda suke yi wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) gani- gani, ba su da cikakkiyar shaidawa cewa shi Manzo ne da ya zo daga Allah, kuma wannan shaidawar it ace rukuni na biyu a cikin rukunnai na shahada. Sun faro asali ne daga wani mutum da ake kira da Zul Khuwaisara at- Tamimiy, Imam al- Bukhari da Imam Muslim sun ruwaito Hadisi (lafazin na Muslim ne) cewa lallai Abu Sa’id al- Khudriy ya ce: Wata rana muna wurin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana raba ganima, sai Zul Khuwaisara, -wanda dan kabilar Bani Tamimi ne- ya zo, sai ya ce: ya Manzon Allah, a yi adalci, sai ya ce: (Kai kuwa kaiconka, wane ne zai yi adalci idan ni ban yi adalci ba, lallai na tabe kuma nay i asara idan har ban yi adalci ba), sai Umar Bn al- Khaddab (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: ya Manzon Allah, ka yi mini izini in sare kansa, sai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ka kyale shi, yana da jama’ar dadayanku zai raina sallarsa idan ya gwama da sallarsu, zai kuma raina azumunsa idan ya gwama da azuminsu, suna karanta Alkur’ani amma ba ya wuce makogwaronsu, suna fita daga addini kamar yadda kibiya take fita daga baka… za su bayyana a lokacin da aka sami rarrabuwa tsakanin mutane) sai Abu Sa’id ya ce: (Wallahi ina shaida cewa na ji wannan bayani daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ina kuma shaida cewa wallahi Sayyiduna Aliyu Bn Abudalib (Allah ya kara yarda da shi) ya yake su, a lokacin ina tare da shi). Lallai wadannan kungiyoyi sun yi ta habaka a fagen tsaurin ra’ayi a tsawon tarihi, ta yiwu ma wasunsu su kafirta wasu, wannan ne abin da ake kira da “has ashen bibiyar al’ummomi”; sakamakon ba su da nagartacciyar madogara, da mafuskanta da za su rinka saita su, alal misali tsaurin ra’ayi ya fara daga Ikhwan, ya zarce zuwa ga salafiyyar jahadiyya, zuwa ISIS da sauransu.

Share this:

Related Fatwas