Makkana addinin Allah

Egypt's Dar Al-Ifta

Makkana addinin Allah

Tambaya

Kungiyoyin ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi suna riya cewa suna aiki ne domin tabbatar da shari’ar Allah Madaukakin sarki da addininsa tsakanin mutane, da fitar da mutane daga duhu zuwa haske, mene ne gaskiyar wannan magana?

Amsa

Lallai Alkur’ani mai girma ya kawo wannan kalma ta “Attamkin” a wurare masu yawa, kaman a inda Allah Madaukaki ya ce: (Shin ma ba su san cewa mun halakar da al’ummomi masu yawa kafin su ba ne, mun fa ba su duka abubuwan da za su sanya su yi karfi, su kuma kafu a bayan kasa, wadanda ba mu ba ku irinsu ba..) [al- An’ami: 6]. Da inda Madaukakin Sarki ya ce: (Wadannan muminan da muka yi alkawarin ba su nasara, su ne wadanda idan muka ba su daman shugabanci a bayan kasa suke kiyaye kyakkyawar dangantakarsu da Allah Madaukakin Sarki, da dangantakarsu da sauran mutane, suna gabatar da Sallah kaman yanda ta kamata, suna kuma bayar da zakkar dukiyoyinsu ga wadanda suka cancanta, suna kuma bayar da umurnin aikata dukan alhairi, suna hana dukan wani abu da yake akwai sharri a cikinsa. Lallai makomar komai yana wurin Allah ne shi kadai, inda yake daukaka wanda ya so, ya kuma kaskantar da wanda ya so daidai da hikimarsa) [al- Hajji: 41]. Da kuma inda yake cewa: (Lallai Allah ya yi wa wadanda suka yi imani da gaskiya, suka kuma yi mata biyayya a cikinku, suka kuma aikata ayyuka na gari cikakken alkawari kuma mai karfi cewa: lallai zai sanya su gaji wadanda suka gabace su a wurin shugabanci, da jagoranci a bayan kasa, kaman dai yanda yake yi wa wadanda suka gabace su. Ya kuma bai wa addinin Musuluncinsu da ya yarda masu da shi a matsayin addini nasara da galaba, ya zama suna da kwarjini da kima, ya kuma sauya halin tsoron da suke ciki ya koma aminci, ta yanda za su bauta mini cikin kwanciyar hankali, ba su kuma hada ni da kowa wajen bauta. Duk wanda ya zabi kafirci bayan wannan alkawari na gaskiya, ko ya yi ridda ya fita daga cikin addinin Musulunci, to kuwa lallai wadannan su ne ‘yan tawaye masu taurin kai da suka kafirce wa Allah) [an- Nur: 55].

Abin lura a cikin wadannan ayoyi da aka bijiro da su shi ne lallai Allah Madaukakin Sarki ya yi amfani da kalmar “Attamkin” wajen hakkokin muminai da wadanda ba muminai ba, da ma hakkokin al’ummomin da suka gabata, kuma aikin a cikin wadannan ayoyin an danganta su ne da Allah mai girma da daukaka, tabbatarwar shi ne yake samar da ita, ya kuma yi ta, ba wai hukunci ne da ya daura akan dan Adam ya samar da shi, ko ya yi aiki domin isa zuwa gare shi ba.

Bayan lura da duba na tsanaki za mu ga cewa rashin bin manhaji na ilimi ne ya sanya wasu suka tarjama ma’anar “Attamkin” da cewa wasu surori ne na daukan matakai, wanda hakan zai ba su dama zuwa ga darewa akan madafun iko idan sun kafirta al’umma, da kuma cewa su ne kawai Musulmai, da riya wajibcin yin aiki domin isa zuwa ga tamkini, wai don dawo da komai zuwa ga bigirensa.

Share this:

Related Fatwas