Mafuskantar ma’anar Hadisin (An umu...

Egypt's Dar Al-Ifta

Mafuskantar ma’anar Hadisin (An umurce ni da na yaki mutanen..)

Tambaya

Da yawan masu tsattsauran ra’ayi –a yayin yi wa mutane ta’addanci– suna dogara da Hadisin (An umurce ni da na yaki mutanen..), shin haka wannan Hadisin yake nufi? kuma mene ne ma ma’anarsa?

Amsa

Wannan Hadisi dai an yi ittifaki akan ingancinsa, kuma yana da madogara masu yawa, lafazin “Annasu” wato (mutane) ba a nufin dukkan mutane da shi gaba daya, babu shakka mu’ahidi da zimmiyi sun fita daga cikin jerin wadanda aka ambata a Hadisin nan, saboda fadin SallalLaHu AlaiHi wa AlihHi wasallam:  “Duk wanda ya kashe kafirin amana to ba zai shaki kamshin Aljanna ba, kuma ana iya jin kamshinta ne kimanin tafiyar shekara Arba’in” [Bukhari].

Sai fa duk wadanda suka fara kawo mana hari, ko yaki daga cikin mutane hakika Allah ya umurce mu da mu kare kanmu wurin mayar da ta’addancinsu gare su, Allah Ta’ala ya ce: (Ku yaki wadanda suke yakanku saboda daukaka kalmar Allah, amma kada ku yi ta’addanci) [Albakara:190], don haka ne Manzon Allah  SallalLaHu AlaiHi wa AlihHi wasallam ya ce a wannan Hadisin, (An umurce ni da na yaki mutanen) ai daga cikin wadanda suke yin ta’addanci, wannan umurni ne aka ba  Manzon Allah  SallalLaHu AlaiHi wa AlihHi wasallam, kuma wanda ya ba shi umurnin shi ne Allah Mai girma da Daukaka, Hadisin (An umurce ni da na yaki mushirikai) na nuni akan wancan Hadisin.

Amma wadanda ba su yake mu ba, to Allah Sabuhanahu wa Ta’ala ya umurce mu da mu  kyautata mu’amala da su, da yi musu adalci, Allah Ta’ala ya ce:(Allah bai hana ku yin mu’amala da wadanda ba su yake ku saboda addininku ba kuma ba su fitar da ku daga cikin gidajenku ba, bai hana ku da ku yi mu’amala da su kuma ku kyautata musu ba Allah yana son masu kyautatawa) [Al’mumtahina: 8] duk wadanda ba su yake mu ba, za mu yi mu’amala da su mu kyautata musu, mu barsu su yi addininsu ba tare da mun hana su ba.

Duk wanda ya fahimci wannan Hadisin sabanin abin da aka ambata a baya, to dan tayar da fitina ne, shin ya so ya kafa hujjar halasta kashe mutane ne baki daya ko kuma ya so sanya kokwanto ne a cikin sunnar Annabi SallaHu AlaiHi wa AliHi wa sallam.

Share this:

Related Fatwas