Azumtar ranar Ashirin da bakwai ga ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Azumtar ranar Ashirin da bakwai ga watan Rajab?

Tambaya

Mene ne hukuncin azumtar ranar Ashirin da bakwai ga watan Rajab?

Amsa

Yin nafilar azumin ranar Ashirin da bakwai ga watan Rajab dai babu hani akansa a shari’ance, ai wannan azumin ma yana daga cikin ayyukan da ake so aka kuma kwadaitar da yi tare da girmama sha’aninsa, saboda fadin Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam: (Duk wanda ya azumci ranar Ashirin da bakwai na watan Rajab Allah zai rubuta masa ladan azumin wata sittin). Wannan Hadisin koda kuwa akwai rauni tare da shi, sai dai ana iya amfani da shi a wurin falala da kwadaitarwa kan aikin alheri kamar dai yanda malamai suka bayyana.

Hakika wasu nassosi sun zo daga malaman fikihu inda suka kwadaitar da azumin wannan rana, saboda da falalar da yake tattare da azumin, domin ya dace da wani lamari mai girma ne a cikin tarihin Musulunci, haka kuma wannan rana tana daga cikin ranaku masu girma da ake son aikata bauta a cikinsu, daga ciki akwai azumi, daga cikin malaman da suka kwadaitar da yin haka akwai: Imam Abu Hanifa, kamar dai yanda Imam Alkarrafi ya nakalto daga littafin “zakhirah” (2/532), da kuma Imam Ibn Habib da wasu daban, kamar dai yanda Allama Khalil ya ambata a littafin “At’taudeh” (2/461), da kuma Imam Ghazali, da Imam Haddab, ai wasu daga cikinsu ma sun bayyana cewa azumtar wannan rana ta Ashirin da bakwai sunna ce, kamar Allama Sulaiman Al’jamal kamar yanda ya zo a littafin “Hashiya ala sharhi manhajil Dullab” (2/249), hakama Allama Shatta Al’dimyadi a littafin “Ianatul Dalibin” (2/306). 

Share this:

Related Fatwas