Uƙubar da Allah Maɗaukakin Sarki za...

Egypt's Dar Al-Ifta

Uƙubar da Allah Maɗaukakin Sarki zai yi wa ƴan ta’adda

Tambaya

Mene ne uƙubar da Allah Maɗaukakin Sarki zai yi wa ƴan ta’adda?

Amsa

Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Tabbas idan munafukai, da waɗanda zukatansu suke cike da cuta, da masu ‘yan yama- ɗiɗi masu yaɗa jita- jita a gari ba su daina ba, wallahi za mu ba ka umurnin ka bi ta kansu, sannan kuma ba za mu bari su cigaba da maƙwabtakar ba sai kaɗan. Tsinannu ne su, a duk inda aka same su a kama su, a yi masu mummunar kisa. Wannan it ace Sunnar Allah da ta faru da waɗanda suka gabata, ba kuma z aka taɓa samun wani sauyi a cikin Sunnar Allah ba) [a- Ahzab: 60 -63],

Malaman tafsiri sun ce: Lallai kalmar “murjifuna’ a wannan ayar tana nufin: waɗanda suke tsoratar da mutane, sannan suke yaɗa labarun tsoratarwa da firgici a tsakanin mutane ta hanyar ƙarya, wannan kuma na kasancewa ne saboda munanan manufarsu ta ƙashin kai, sannan sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ambaci adadin uƙubar da zai yi musu matuƙar ba su tuba, sun bar waɗancan munanan ayyukan nasu ba.

Uƙubarsu ta farko ita ce: tona masu asiri da kunyata su, wannan yana daga cikin ma’anar “La nugriyannaka” abu na Biyu kuma shi ne: kaɗa su da korarsu daga cikin al’umman da suke rayuwa a cikinsu, na Uku kuma shi ne: la’antarsu, wato nesanta su daga rahamar Allah Maɗaukakin Sarki, na Huɗu kuma shi ne: kashe duk wanda ya ɗauki makami daga cikinsu, wato wannan yana nuni ne kan halaccin yaƙarsu, sannan sai Allah Maɗaukakin Sarki ya bayyana cewa: Lallai waɗannan uƙubobin da za a yi wa irin waɗannan mutanen a cikin al’umma na daga cikin sunnoninsa waɗanda ba sa sauyawa,  kuma ba a shafe su.

Share this:

Related Fatwas