Hatsarin da ke cikin “Tunanin mai t...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hatsarin da ke cikin “Tunanin mai tsattsauran ra’ayi”

Tambaya

Mene ne alamomin da suke tattare da hatsarin da kungiyoyin masu kafirta mutane suke yiwa al’umma?

Amsa

Yana daga cikin abin da babu shakka a cikinsa cewa fahimtar addini a karkace  yana daga cikin abubuwa mafiya hatsari da muke fuskanta a cikin kasashenmu da kuma waje, saboda shi tsattsauran ra’ayi na addini – a bisa al’ada – ba ya tsayawa ga wani tunani mai tsauri wanda yake zaman kansa wanda ke tankware a sasanninsa, kai daga nan ma lamarin ke hauhawa zuwa ga kokarin farlanta ra’ayinsa ga mutane tare da daure al’umma baki dayansu da wannan tsattsauran ra’ayin nasa bisa tilasci, to a irin haka fa babu wata hanya sai tsattsauran ra’ayi  da ta’addanci da zubar da jini kamar dai yanda ake ganin hakan zahiri ga kungiyar ‘yan’uwa na ‘yan ta’adda.

Dukkan wadannan lamuran da aka ambata a baya - duk da cewa suna faruwa – amma sai fa suna kasancewa ne kamar wasu matakai ne na farko farko daga cikin abubuwa da su wadancan mutanen suke fatan ganin ya tabbata,  hakika burace buracen ‘yan ta’adda ya fadada wanda har hakan yakai ga samun kudade da samar da sojoji da baiwa bataliyoyinsu makamai da kuma jan ra’ayin matasa da ba su horo na yaki da sanya su a cikin jerin bataliyoyinsu, da kuma yanda suke amfani da dukkan hanyoyin fasaha da kafofin sadarwa na zamani domin yada akidarsu na tsattsauran ra’ayi, tare da jan ra’ayin matasa masu jini a jika domin jefa su cikin yanayi na kunar bakin wake.

Share this:

Related Fatwas