matsalar yin matsin lamba

Egypt's Dar Al-Ifta

matsalar yin matsin lamba

Tambaya

Ta wace fuska yin matsin lamba da kuma tunanin saukar ukubar Allah take yin tasiri a wurin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi?

Amsa

Sarkakiyan da ke tattare da yin matsin lamba alama ce da take zama dole ga mai tsattsauran ra’ayi domin samun daidaiton yanayi a tare da shi,  domin halin mai tsattsauran ra’ayi da tunaninsa na samun tarnaki a wurin da yake rayuwa, kai irin wannan nuna karan tsanar akansa na iya kaiwa har ga danginsa, domin mai tsattsauran ra’ayi ya samu mafita daga mayar da shi saniyar ware a cikin al’umma sai ya rinka jin a ransa cewa yana cikin matsin lamba ne,  kuma shiga cikin irin wannan yanayin sunna ce, domin shi mai riko ne da addininsa, kuma shi mai riko da addininsa kamar dai “wanda yake rike da garzashin wuta ne” kuma saboda kasancewarsa mai riko da addini to fa lallai al’ummarsa “jahila ce” dole ta nuna masa kiyayya da tsangwama a duk sanda damar hakan ta samu.

Saboda haka ne mai tsattsauran ra’ayi – a koda yaushe – yake bukatar hujjoji akan ingancin hanyar da yake bi na addini, kuma duk wanda yake bin wata hanya da ba irin ta sa ba to batacce ne, shin ya kasance ya aminta da fahimtarsa ko a a, don haka ne ma za mu ga ‘yan ta’adda su na da wata fahimta na samuwar ukubar Allah tare da alakanta ta da duk wani yanayi da suka tsinci kansu a ciki don kasancewa wata hujja akan tafarkin da su ke bi, misali kungiyar ISIS bayan bullar cutar korona a China, sannan da kuma bullarta a wasu kasashen Turai kamar Italita da Spain sai suka fitar da wani bayani wanda yake bayyana cewa wannan annobar wata azaba ce mai radadi daga Allah “Ga al’ummun kiristoci” wanda hakan yazo ne kafin cutar ta bazu a kasashen duniya, a cikinsu kuwa har da dukkannin kasashen musulmai.

Share this:

Related Fatwas