Ta’amuli da bankuna
Tambaya
Mene ne hukuncin bai wa banku hayar gida?
Amsa
Bayar da hayar gidaje –ta hanyar yarjejeniyoyi mabambanta- ga bankuna, da karban kudin hayar daidai yake da kowane irin tsarin haya da shari’a ta halatta, haka ma samun amincewa akan kudin hayan abu ne da shari’a ba ta hana ba; saboda hakan yana cikin hakkokin da suka biyo bayan halattaccen kasuwanci, kuma abin da kowa ya sani ne cewa asali a cikin dukan yarjejeniya da mu’amaloli a Musulunci shi ne halacci, muddin ba a sami wani dalili ne na shari’a da ya haramta ba, shi kuwa haya ya halatta ne da dalilai daga littafin Allah da Hadisai da Ijma’in malamai.