Karanta surorin Alsajda da Al’insan a sallar Asuba.
Tambaya
Mene ne hukuncin lizimtar karanta surorin Alsajda da Al’insan a sallar Asuba ranar Jumu’a?
Amsa
Dawwama wurin karanta surorin Alsajida da Al’insan a sallar Asuba ranar Jumu’a yana daga cikin sunnonin da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake aikatawa, kuma yake yawaita aikatawa.
Allah Madaukakin Sarki ne masu sani.