Tsarin cinikayya na Munakasat

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsarin cinikayya na Munakasat

Tambaya

Mene ne hukuncin shiga tsarin munakasat na bai daya ko na kashin kai tare da biyan kudi akan haka?

Amsa

Shi tsarin cinikayya na “munakasa” halas ne a shari’ance, kwatankwacinsa kamar “muzayada” ne, don haka ake dabbaka masa hukuncin munakasa akan hukuncin muzayada, babu laifi a cika sharudan biyan kudin shigowa da kayan matukar bai zarce kimar kudin aikin da akayi akansa ba, saboda shi ne kudin aikin na asali.

Munakasa dai wata hanya ce da ta shahara wurin kulla ciniki na gudanarwa da cibiyoyin gwamnati ke gudanarwa da mutane masu zaman kansu, kamar biyan kudin fito da na kwangila, wani irin tsari ne sabo na mu’amala da kudade, wanda ke son sayen kaya ke aikatawa, ko kuma mai bukatar wani abu na musamman domin samun saukin farashi, to kulla irin wannan cinikin halas ne a shari’ance, kwatankwacinsa shi ne tsarin muzayada, don haka ake dabbaka hukuncinsa akan munakasa, domin haka duk hanyoyin da ake bi wurin kulla cinikin munakasa, na rubutawa da tsarawa da sharuda na gudanarwa ko na dokoki to ya wajaba kar ya ci karo da hukunce- hukuncen shari’ar Musulunci, babu laifi a biya kudin fito, - kimar abin da aka rubuta na sharuda – amma kar kudin ya zarce na asalin kayan da za a shigo da shi.

Share this:

Related Fatwas