Kiran da Musulunci ya yi wurin girm...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kiran da Musulunci ya yi wurin girmama ma’abota kwarewa a fagen ilimi

Tambaya

Shin ya wajaba a rinka tambayar ma’abota sani na ilimi akan abin da suka kware akwai na ilimi da sani?

Amsa

Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya koya mana girmama kwararrun masana a fagen ilimi, duk da sanin da Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) yake da shi daga Allah amma ya kasance yana shawartan ma’abota sani da kwarewa akan lamura daga cikin sahabbai cikin lamuran duniya domin ya koya mana yanda ake mayar da lamari ga masaninsa, Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya kasance yana nuni zuwa ga kwarewar sahabbansa masu girma domin yaba musu akan haka, yana cewa: (Mafi jinkan al’ummata Abubakar, wanda yafi tsananin riko da addin Allah Umar, - Sai Affan ya ce awani karan: Cikin lamarin Allah,- Wanda kuma yafi su matukar kunya Usman, Wanda kuma yafi sanin ilimin gado shi ne Zaid bin Thabit, Wanda yafi kowa kwarewa a wurin karatun Alkur’ani kuma shi ne Ubayyu bin Ka’ab, Wanda kuma yafi kwarewa wurin sanin halar da haram shi ne Mu’azu bin Jabal, Ku sani a cikin kowace irin al’umma akwai amintaccenta, to amintaccen wannan al’umma shi ne Abu Ubaida bin Jarrah) Ahmad.

A cikin wannan hadisin akwai fadakarwa ga mutane domin su kasance a fadake wurin sanin muhimmancin kwarewa a fannoni domin mabukata sanin fannin nasu su koma zuwa garesu ya yin bukata, ko kuma don karkata zuwa ga ma’abocin sanin a lokacin da aka samu cin karo da juna na lamura.

Share this:

Related Fatwas