Mene ne hukuncin mace ta shiga cikin aikin bayar da fatawa tare sauran ayyukan bincike na ilimi?
Tambaya
Mene ne hukuncin mace ta shiga cikin aikin bayar da fatawa tare sauran ayyukan bincike na ilimi?
Amsa
Mace ta na aiki a hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar, inda ake bata damar yin aikin bisa kwarewarta da iliminta.
Lallai babu shakka samun damar yin aiki na bayar da fatawa tare da cikan sharuda na ilimi ba ya zama laifi ga mata su yi, daga cikin abu mafi bayyana akan haka shine iyayen muminai, kamar su Sayyidah Aisha da Sayyidah Hafsat da Sayyidah Ummu Salamata Allah ya yarda da su.
Hakika malamar fikihu ta mazhabar Hanafiyya Fatima ta kasance ta na bayar da fatawa tare da mahaifinta Ala'ud deen Sarmakandi Al-Hanafi, da kuma mijinta Imam Kisa'i Al-Hanafi (dukkansu su uku).