Hukunce- hukuncen jahadi a fikihun Musulunci da dokoki tare da yarjeniyoyin kasa da kasa.
Tambaya
Shin bambance- bambancen da suke tsakanin sashen hukunce- hukuncen jahadi a fikihun Musulunci da dokoki tare da yarjejeniyoyin kasa da kasa yana lalata hukuncin? To mene ne ka’idar yin haka?
Amsa
Bambance- bambancen da suke tsakanin sashen hukunce- hukuncen jahadi a fikihun Musulunci da dokoki tare da yarjejeniyoyin kasa da kasa ba ya yin tasiri akan wadancan dokokin ta kowani irin hali, saboda su wadancan hukunce hukuncen ijitihadi ne kawai da suke dacewa da zamani da yanayin da aka tsinci kai a ciki, idan lokacin ya sauya, ko yanayin ya sauya, to fa dole su ma hukunce- hukuncen su sauya, don haka ne ma za mu ga malaman wannan zamanin ba su nuna rashin amincewarsu akan wadancan dokoki da yarjejeniyoyin ba, ai ma albarka suka sanya musu, sannan suka yi gaggawa zuwa gare su, akasin wadanda suke daukar iliminsu daga littafai fikihu kawai, ba tare da sun zauna gaban malaman ba, mai ya kai fadin wani cikin malamai dadin ji inda ya ce: “Wanda littafinsa ya kasance shehinsa, to kuskurensa zai rinjayi daicewarsa!”.
Amma abin da yake iya yin tasiri akan dokoki da yarjejeniyoyin har a yi musu kallon lalatattu shi ne kawai su saba wa hukuncin shari’a karara bisa abin da babu sabani a cikinsa tsakanin malaman fikihu, a hukuncin jahadi kuma babu wani abu da yake tabbatacce illa asalin shar’anta shi a Musulunci, wanda kuma hakan ya tabbata ne da nassin Al-kur’ani da Sunna domin kare kai, amma sasannin jahadi abu ne da ke iya sauyawa saboda yanayi na sauyawan zamani da wuri da kuma lura da halin da Musulmai ke ciki da abokan gabansu.