Tirsasa iyaye su kula da lafiyar ‘y...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tirsasa iyaye su kula da lafiyar ‘ya’yansu

Tambaya

Mene ne hukunci tirsasa iyaye su kula da lafiyar ‘ya’yansu?

Amsa

Kulawa da lafiyar ‘ya’ya abu ne da shari’a ta wajabta akan iyaye, ko wanda yake jibintar al’amurran kulawa da su; sam bai halatta su yi rikon sakainar kashi, ko nuna halin ko in kula da haka ba duk runtsi, a cikin abubuwan da suka wajaba su bibiya akwai alluran riga- kafi da hukumomin da abin ya shafa suka gabatarwa; saboda ya tabbata cewa bin ire- iren wadannan hanyoyi yana bayar da kariya daga kamuwa da cututtukan da ake jin tsoron kamuwa da su; wannan kuwa saboda aka kiyaye rayuwarsu, da jikkunansu daga cututtuka, a kuma kiyaye al’umma daga dauka nauyin abubuwan da za su biyo bayan haka na yin magani, da kudaden da ake kashewa akan haka.

Share this:

Related Fatwas