Juya mahaifa

Egypt's Dar Al-Ifta

Juya mahaifa

Tambaya

Mene ne hukuncin aikin juyar da mahaifa?

Amsa

Juya mahaifa, ko rufe shi ba tare da wata lalura ba haramun ne a shari’ar Musulunci; saboda wofintar da wani sashe ne na jikin dan Adam ba tare da wani dalili ba.

Amma idan akwai dalili, ko lalurar da zai sanya a yi wannan aiki na juya mahaifa ko rufe shi; kaman idan an ji tsoro kada matar ta halaka ta rasa rayuwarta, ko lafiyarta zai shiga cikin wani mawuyacin hali idan ta sake daukan ciki a nan gaba, ko ya zama akwai wata cuta ta gado da ake tsoron ta shafi jaririn, tare kuma da cewa babu wata hanya ta gyara, ko ta hana daukan cikin, kuma amintaccen likita ne kuma kwararre ya bayyana haka, a ya halatta a gabatar da aikin juya ko rufe mahaifa a cikin irin wannan yanayi.

Allah shi ne masani

Share this:

Related Fatwas