Nuna kyama

Egypt's Dar Al-Ifta

Nuna kyama

Tambaya

Mene ne hukuncin nuna kyama?

Amsa

Dukan nau’o’in nuna kyama abubuwa ne da shari’a take zarginsu, dokoki kuma sun sanya su a matsayin laifuffuka, domin zalunci ne da yake cutar da mutanen da ake nuna masu kyama da wariya, bugu da kari kuma hakan barazana ne ga tsaro na zamantakewa, ganin cewa yin hakan laifi ne, hukumar bayar da fatawa ta Misra tana kira zuwa ga daukacin al’umma da su fito su yi wa wannan dabi’a burki, su kawo karshenta, tana kuma daura wa hukumomin ilimi da na da’awa da kafafen yada labarai alhakin da ya rataya akansu, na su fito su taka rawar da ta dace da su, ta hanyar bayyana hatsarin da yake tattare da wannan tada, da wayar da kai game da ita; su dasa dabi’ar kiyaye jin wasu, da hakkokinsu da mutunta su.

Share this:

Related Fatwas