Rufe mamaci

Egypt's Dar Al-Ifta

Rufe mamaci

Tambaya

Mene ne ka’idojin da shari’a ta sanya wajen rufe mamaci?

Amsa

Rufe mamaci farali ne na kifaya (watau wanda ya rataya akan daukacin al’umma), abin da ake bukata a kabarin da shari’a ta amince wanda ya inganta a rufe mamaci a ciki shi ne: ya zama ya samar da cikakken karrama jikin dan Adam bayan ya rasu, ya kuma kiyaye shi daga duk wani wuce gona da iri, ya kuma suturta sauyin da yake bijiro masa, a cikin abubuwan da suke da jibi da rufe mamaci, akwai abubuwa da suka rataya da mamaci kamar abubuwa  masu zuwa:

Mustahabi ne a shigar da shi kabarin ta hannun dama.

Wajibi ne a fuskatar da fuskar mamaci da kirjinsa da cikinsa zuwa ga alkibla, haramun ne a fuskantar da fuskarsa ta wurin da ya saba da alkibla.

Babu laifi a rufe shi da rairayi, ko turbaya, duka sun halatta.

Share this:

Related Fatwas