Murna da bala’in da ya auka wa wani...

Egypt's Dar Al-Ifta

Murna da bala’in da ya auka wa wani

Tambaya

Mene ne hukuncin murnar da bala’in da ya auka wa wani?

Amsa

Murna da bala’in da ya sauka wa wani mutum, Kaman mutuwa, ko waninsa sifa ce mai muni, saboda haka bai halatta ba a Musulunci.

Lallai yin murna da bala’in da ya auka wa wani, sawa’un mutuwa ce ko waninta cikin masifu abu ne da shari’a ta hana shi yi, hasali ma sifa ce mai matuqar muni, da zukata masu tsabta suke kyamata, masu mutunci kuma suke nesanta, an ruwaito Hadisi daga Wasilat Bn al- Asqa’u (Allah ya kara yarda da shi) daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Kada ka bayyana murna da bala’in da ya faru da dan uwanka, sai Allah ya fitar da shi, kai kuma ya jarrabe ka) [al- Trmiziy]. Sunnar Allah a cikin rayuwa ita ce babu wanda yake tabbata akan yanayi da hali guda daya; lallai rayuwa ana yinta wata rana a sha zuma wata rana a sha madaci, kuma mutuwa daya ce daga cikin abubuwan da Allah ya kaddara wa daukacin halitta, babu wani mutum da ba zai mutu ba; saboda haka bai kamata wani ya yi murnar mutuwar waninsa ba, babu wanda ya isa ya guje wa mutuwa, komin tsawon ran da ya yi, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Kowane rai zai dandana mutuwa) [Ali Imran: 185].

Share this:

Related Fatwas