Munana mu’amala da matar aure

Egypt's Dar Al-Ifta

Munana mu’amala da matar aure

Tambaya

Mijina yana munana mu’amala dani, mene ne hukuncina?

Amsa

Duk abin da miji ke aikatawa na munanawa ga matarsa to wani abu ne wanda bai kamata ba a shari’ance, domin musulunci ya umurci miji da ya kyautata zamantakewar aure, inda Allah Madaukakin Sarki ya bayar da labari na zamantakewar aure cewa ta ginu ne akan natsuwa da kauna da tausayi, Allah Ta’ala yana cewa: (yana daga cikin ayoyin ni’imar Allah gareku halitta muku mataye daga jikunanku domin ku samu natsuwa dasu, sannan ya sanya kauna da tsausayi a tsakaninku lallai a cikin wannan akwai abin lura ga mutanen da suke yin tunani) {Rum:21}, sannan  Annabi  SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya sanya alamar alheri na zamantakewar aure bisa kyautatawa iyalai, an karbo daga Sayyidah Aisha Allah ya kara mata yarda cewa Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Mafi alherinku sune masu kyautatawa iyalansu, to nine mafi alherinku wurin kyautatawa iyalaina) Tirmizi.

Allah Madaukakin Sarki shine mafi sani.

Share this:

Related Fatwas