Sayen gidaje kafin a gina su

Egypt's Dar Al-Ifta

Sayen gidaje kafin a gina su

Tambaya

Mene ne hukuncin sayen gidaje kafin a gina su?

Amsa

A cikin muhimman manufofin shari’ar Musulunci akwai samar da maslaha ga bayin Allah da kuma kawar da duk wata cuta da take fuskantarsu, domin asali a cikin dukan mu’amaloli da aka gina su akan ‘yar da juna shi halacci, matukar hakan bai ci- karo da nassi na shari’a ba; hakan ya kasance ne saboda irin yanda bukatun mutane yake. A cikin waxannan ma’amaloli akwai yarjejeniyar sana’antawa, lallai kamfanonin da suke yin wannan aiki sukan dauki alhakin gina gidaje akan wani sanannen sifa da suke yin ittifaki akanta tsakaninsu da mai saye, wannan zai sanya sifar da aka gina cinikayya akanta a cikin sharuddan kasuwancin a fili take karara, saboda haka sayen gidaje kafin a gina su shi ne yarjejeniyar sana’antawa, hakan kuma yana cikin abubuwan da mutane suka saba da shi, suke kuma gudanar da mu’amalolinsu akansa; wannan  ya halatta idan sharuddan haka suka samu, ma’ana ya zama babu rashin sani, ko rudi, ya kuma zama a iyakance lokaci, da sani kudinsa, da hanyoyin da ake bi wajen biya, shi ma saboda guje wa rikici da sabani a nan gaba.

Share this:

Related Fatwas