Mamaye filayen noma domin yin gini....

Egypt's Dar Al-Ifta

Mamaye filayen noma domin yin gini.

Tambaya

Mene ne hukuncin mamaye filayen noma domin yin gini?

Amsa

mamaye filayen noma domin yin  gini a wurin bai halasta ba a shari’ance, saboda hakan zai kai zuwa ga cutarwa mai girma, saboda hakan zai haifar da cutarwa mai girma, hakanan hakan ya sabawa kwadaitarwar da shari’a tayi na shukawa da dasawa a wurare, a cikin sahihaini an karbo daga Anas Allah ya kara masa yarda, ya ce: Manzon Allah sallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce: (Babu wani musulmi da zai dasa wata bishiya, ko ya shuka wani shuka, sai wani tsuntsu yaci ko wani mutum ko wata dabba, face ya samu ladan sadaka da hakan).

Filaye na noma su ne ginshikan tattalin arzikin Masar, yin gini a cikinsu wuce gona da iri ne, kuma barnatar da arzikin noma ne a Masar, kuma gabatar da bukatar mutane bisa lura da abin da zai amfanesu, to ya wajaba a fadakar wurin ganin barna bai shiga ciki ba, ta hanyar yin gini a filayen da aka ware domin noma, wanda hakan zai taimaka wurin raunata tattalin arzikin kasa.

Share this:

Related Fatwas