Rufe kafar mace a lokacin sallah.

Egypt's Dar Al-Ifta

Rufe kafar mace a lokacin sallah.

Tambaya

Mene ne hukuncin rufe kafar mace a lokacin sallah?

Amsa

Abin da ya wajaba ga mace shi ne ta rufe dukkannin jikinta a lokacin da take yin sallah, in banda fuskarta da tafin hannuwanta, an karbo daga Umar bin Khaddab Allah ya kara masa yarda ya ce: (Mace tana yin sallah ne cikin zannuwa guda uku: gyale da dankwali da majanyi).

Amma mace ta rufe kafafunta a lokacin sallah kuwa wani abu ne da aka samu sabanin malamai akan haka.

Daga cikinsu akwai wanda ya ce dole ne mace ta rufe kafafunta, saboda hadisin Ummu Salamata Allah ya kara mata yarda cewa wata mata ta tambayeta akan tufar da ya kamata mace tayi sallah dashi, sai tace mata: (zata yi sallah ne da gyale da majanyin da zai sauka ya rufe kafafunta), ai zanin da zai suturta bayan kafafunta.

Daga cikin malamai kuma akwai wanda ya ce halas ne mace ta bude kafafunta a lokacin sallah, saboda shari’a ta togace wuraren  adon mace, kamar fuskanta da tafin hannuwanta da kafafunta, Allah Ta’ala ya ce: (Ba sa bayyana adonsu sai dai fa abin da ya bayyana daga cikin wuraren adonsu)[Nurr:31]

Amma abin da yafi bayyana shi ne wanda aka bayar da fatawa akansa na halascin yayewan kafar mace a sallah, domin saukaka mata lamura da cire mata nauyi da yawa akanta, idan mace tayi sallah alhali kafarta a bude suke to sallarta tayi.

Share this:

Related Fatwas