Ma’anar sadakatul jariya, da kofofinta
Tambaya
Mene ne ma’anar sadakatul jariya, da kofofinta?
Amsa
Sadaka jariya ita ce sadakar da ta cigaba da wanzuwa a cikin al’ummomi masu zuwa, ba wai kawai a cikin al’umma daya ba, ita ce wadda ta game mutane masu yawa, ba wai mutum daya ba, kaman buga Alkur’anai, da litattafan ilmomi masu amfani, da gina masallatai, da makarantu da asibitoci, da gina makabartu ga masu bukata, da bayar da gudummuwa a cikin manyan ayyukan hukumomi da suke isar da ruwa da wutar lantarki, da hidimomi ga mabukata, da makamanta haka, abubuwan da suke biyan bukatun mutane a koda yaushe, amfaninsu kuma yake isa ko’ina da ina.