Satar fahimta da sana’a
Tambaya
Mene ne hukuncin satar fahimta da sana’a?
Amsa
Satar fahimta da sana’a a kowane fanni abu ne da shari’ar Musulunci ta haramta, saboda haka shari’ar Musulunci tana bayar da kariya ga mallakar fahimta da tunani, kaman yadda take kare mallaka abubuwa; akwai cutar da hakkokin mutane a tattare da satar fahimtarsu da tunaninsu, kuma Musulunci ya haramta cutarwa; saboda maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Babu cuta babu cutarwa) [Ahmad da Ibn Majah], da kuma maganarsa mai tsira da aminci (Muslmi shi ne wanda mutane suka tsira daga barin harshensa da hannunsa) [Ahmad a cikin al- Musnad].
Daga nan ne doka ta kiyaye mallakar tunani ga masu shi a wadannan fagage, ta kuma tanadi hukuncin da zai zama izina ga dukan wanda ya cutar da mutane a fahimta da tunaninsu.