Hukuncin fadin “Haraman” bayan idar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin fadin “Haraman” bayan idar da sallah.

Tambaya

Mene ne hukuncin fadin “Haraman” bayan idar da sallah?

Amsa

Fadin da wasu masallata sukeyi ga sashensu bayan idar da sallah na cewa: “Haraman”yana daga cikin kofofin addu’a, ma’anarsa shi ne: Ai ina maka fatan kayi sallah a harami, shi dai addu’ar masallata ga sashensu bayan idar da sallah ta hanyar yi wa juna addu’oi abune mai kyau da aka shar’anta, bai halasta a karhanta haka a shari’ance ba, saboda shidai yin addu’a abune da aka halasta, yin addu’a bayan idar da sallah abu ne da yake tabbatar da halascinsa na asali, tare da tsananta son ayi hakan, idan har musulmi ya yi wa dan’uwansu musulmi addu’a, to dalili ne na alamun amsar addu’ar, akan haka ne ma al’adar musulmai ta kasance a baya da yanzu, musanta haka kuma ko bidi’antar da mai aikata hakan alama ce ta tsanantawa da tsaurarawa irin wanda Allah da Manzonsa SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam basa son haka.

Share this:

Related Fatwas