Yin magani “rukiyya” da Alkur’ani Mai girma.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin “rukiyya” da Alkur’ani Mai girma.
Amsa
Ya halasta ayi magani da Alkur’ani Maigirma domin samun waraka daga kowani irin ciwo, tare da yin kuduri a zuciya kan cewa yin maganin ba shi da wani tasiri akaran kansa, abinda ake kudurtawa shine mai warkarwan shine Allah Ta’ala, tare da girman ludufinsa da ikonsa, kuma ya kamata mu kiya yi makaryata ‘yan wanki, wadanda suke cutar mutane, su na amsar kudadensu da sunan su masu yin magani ne, mafi dacewa shine mutum ya yi wa kansa maganin ko ya nemi hakan daga mutane nagartattu, irin wadanda aka san su da aminci.
Tare da wannan akwai bukatar sanin cewa dole a dauki matakan samun lafiya da waraka ta wasu hanyoyi na daban, wadanda Allah Ta’ala ya sanya su a matsayin dalilai na samun waraka daga cututtuka.