Fifiko tsakanin tsawaita karatu a tsayuwar dare da kuma yawaita adadin raka’oi.
Tambaya
Wanne ne mafi dacewa, a tsakanin tsawaita karatu a sallar tsayuwar dare a yawaita adadin raka’oi?
Amsa
Sashen malaman fikihu suna ganin cewa tsawaita karatu a sallar tsayuwar dare shine mafi dacewa daga yawaita adadin raka’oin da mutum kan yi, ya yin da wasu kuma suke ganin yawaita adadin raka’oi shine mafi dacewa.
Amma mu anan abinda muke bayar da shawara akai shine: mutum ya cigaba da yin abinda yafi samun natsuwa akai, sannan yafi samun khushu’i a ciki, shin a tsawaita sallar ne da karatu, ko kuma a yin adadin raka’oi ne, da yawaita su, tare da yawan lizimtar bin hanyoyin da suka dace wurin gudanar da sallar a cikin jama’a a masallatai, domin kar a samu matsala a masallatai, saboda hakan ya dace da manufofin shari’a.