Kiran sallar Juma’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Kiran sallar Juma’a

Tambaya

Sau nawa ake kiran sallar Juma’a?

Amsa

A asali ana kiran sallar Juma’a ne a lokacinta, idan liman ya zauna akan mimbari, wannan shi ne ya dace abin da ake aiki da shi a zamanin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ya kuma dace da yanayinsu, shi kuwa dayan kiran sallar sunna ne mai kyau da halifan Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya sunnanta, watau sayyiduna Usman Bn Affan (Allah ya kara yarda da shi) a lokacin da mutane suka yawaita, da nufin ya fadakar da su ta yanda za su halarta kafin liman ya hau kan mimbari, kuma haka Musulmai suka hadu a kai, suke aiki da shi ba tare da wani ya yi inkari ba, an ruwaito Hadisi daga Sa’ib Bn Yazid (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: (Da ana yin kiran sallah a ranar Juma’a ne a farkon lokacinta, idan liman ya zauna akan mimbari a zamanin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da zamanin Abubakar da Umar (Allah ya kara yarda da su), a zamanin Usman (Allah ya kara yarda da shi) mutane sun kara yawa, sai aka kara kiran sallah na uku, a zamanin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) kiran sallah daya ne) [al- Bukhari].

Sam bai kamata a yi amfani da ire- iren wadannan mas’aloli na sabani wajen tayar da fitina da rikici a tsakanin Musulmi ba, wajibi ne a bi abin da hukumomin da abin ya shafa suka tsara.

 

Share this:

Related Fatwas