Hukuncin yin sallar nafila a cikin ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin yin sallar nafila a cikin jam’i.

Tambaya

Mene ne hukuncin yin sallar nafila a cikin jam’i?

Amsa

Malaman fikihu sun yi ittifaki akan sunnancin yin sallolin idi da na khusufin rana ko wata, da kuma na rokon ruwa da tirawihi a cikin jam’i, sai dai sun yi sabani akan sallolin nafila, bayan wadanda aka ambata, don malaman mazhabobin Hanafiyya da Malikiyya sun tafi akan cewa asalin yin salloli na nafila shine ayi su daban-daban kuma a boye, an karhanta taruwan jama’a a sallolin nafila, idan ya zama ana yin hakan domin jiran mutane su taru saboda yawansu, Malikiyya ma sun kara da cewa: Ba a son taruwar mutane domin yin sallar jam’i musamman a wuri bayyananne, ko da kuwa masu yin sallar ba su da yawa, malaman fikihu na Shafi’iyya da Hanbaliyya sun tafi zuwa ga cewa, ya halasta ayi sallar nafila a cikin jam’i kuma ba tare da karhanci ba.

Saboda haka, gwargwadon abinda malaman fikihu su ka tsaya akai shine sallar nafila a cikin jam’i ta inganta, sabanin malamai akan haka kawai shine kasantuwar an karhanta hakan ko ba a karhanta ba, wannan lamari ne wanda yake da yalwa sosai, idan mutum yaga cewa zuciyarsa ta natsu da yin sallar nafila a cikin jam’i to ya yi, domin babu komai a gareshi.

Share this:

Related Fatwas