Hukuncin gina butun-butumi na mutum...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin gina butun-butumi na mutum da kuma dogon yaro

Tambaya

Mene ne matsayin  musulunci akan gina butun-butumi na mutum da kuma dogon yaro?

Amsa

Girmama shahidai a duniya kamar dai yanda ake kira da "butum-butumi na dogon yaro" abu ne wanda yake halas a shari'ance, kuma wannan ya shiga cikin jerin nassosin da suke tabbatar da daukakar wanda ya yi shahada a wurin Allah, kamar dai yanda yanzo a cikin fadin Allah Ta'ala: (Wandanda suke yiwa Allah da Manzo biyayya to irin wadanan su ne suke kasancewa tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a garesu daga cikin Annabawa da masu gasgatawa da wadanda suka yi shahada da salihai tafiya a layin wadannan ta  kyautata).{Nisa'I 69} 

Akan sanya shahidai a cikin zukata a koda yaushe cikin al'umma, ta yanda sunayensu ba sa fakuwa a cikin zukata, ba don komai ba sai don an san matsayinsu a wurin Allah, kuma hakan yana bayyana girman abinda suka gabatarwa al'umma a kasashensu, domin tabbatar da sakayya garesu, sannan kuma domin tabbatar da abinda yazo a cikin nassosi na Alkur'ani Mai girma na girmama su, tare da tabbatar da dawwamarsu a cikin rayuwa, da tabbatar da rayukansu, da kuma bayyana matsayinsu na shahada, Allah Ta'ala yana cewa: (ka da ku yi zaton wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne  ai su rayayyu ne ana azurtasu a wurin ubangijinsu, su na yin farin ciki da abinda Allah ya ba su daga cikin falalarsa kuma su na yin albishir ga  wadanda ba su riga sun riske su a tafarkin shahada ba a bayansu cewa babu tsoro a garesu kuma babu bakin ciki, su na yin albishir da irin ni'imar da Allah ya yi  mu su da kuma falalarsa akansu kuma lallai Allah ba ya wofintar da sakamakon da muminai suka samu na aikinsu) {Ali Imran:169}.

Share this:

Related Fatwas