Dauke Mus-hafi daga masallaci.

Egypt's Dar Al-Ifta

Dauke Mus-hafi daga masallaci.

Tambaya

Mene ne hukuncin daukar mus-hafi daga masallaci?

Amsa

Duk wani abu da ya kasance wakafi ne ga masallaci to bai halasta a fitar da shi daga masallacin ba, shin anyi wa mutum izinin fita da abun ko ba a yi masa ba, duk wanda ya dauki wani abu kamar mus-hafi da aka ajiye don karantawa, to ya wajaba ya mayar da shi, idan kuma ya yage ko ya bata to ya wajaba mutum ya kawo madadinsa sannan ya nemi Allah tuba akan abin da ya aikata. 

Share this:

Related Fatwas