ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) ƙungiya ce ta masu aikata laifuffukan zubar da jini ba halattacciya ba ce
Tambaya
Shin ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) halattacciyar ƙungiya ce da take magana da sunan Musulunci?
Amsa
ISIS ƙungiya ce ta masu aikata laifuffukan zubar da jini, ba halattacciya ba ce da take magana da sunan addinin Musulunci, hasali ma Musulunci ya haramta ayyukan da take yi, ya kuma tanadi azaba mai tsanani a duniya da lahira ga waɗanda suke aikata ire- iren waɗannan ayyuka.
Hakan ya kasance ne saboda addinin Musulunci addini ne na zaman lafiya, da tsaro, da rahama ga ɗaukacin halittun Allah; bai taɓa tsayuwa, ko ginuwa akan zubar da jini, ko tsorata mutane da sanya su cikin razani ba, wannan ne kuma akasin abin da ISIS take aikatawa na yunƙurin tabbatar da ƙaryar halifanci da take riyawa a mahangarta, wanda sam –sam bai yi daidai da manyan manufofin Shari’ar Musulunci ba ta fuskoki masu yawa:
Ma’anar Halifanci kanta ta sami sauye- sauye tun daga zamanin Hilafa Rashida zuwa wannan zamanin da muke ciki; lura da ƙarnoni masu yawa da suka wuce, da kuma ƙara faɗaɗa da yaɗuwar Musulunci, da ƙaruwar adadin Musulunci, saboda haka babu wani halifa guda ɗaya da yake jagorantar ƙasashen Musulmai; yanzu kowane yanki daga cikin yankuna suna da shugaba, ko sarki da yake shugabantarsu.
Yanda suke aiwatar da gurɓatacciyar fahimtarsu game da ma’anar jahadi, inda suke adawa da shugabanni da suke jagorancin al’umma, suke kuma kashe Musulmai, da ribatar matansu, ta halatta cin dukiyoyinsu ta hanyar zalunci da ta’addanci, wanda dukan ƙasashe, ko garuruwan da suka ƙwata suka mayar da su ƙarƙashinsu, shaidu ne akan waɗannan laifuffuka da ISIS take aikatawa.
Ayyukan da ISIS take aikatawa ɓarna ne a bayan ƙasa ba tare da haƙƙi ba, kuma dole ne a zartar da hukunci da haddin “Haraba” akansu, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Shi kawai uƙubar waɗanda suke yaƙar Allah Maɗaukakin Sarki da Manzonsa (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) idan suka yi wa tsarin shugabanci da hukunce-hukuncen shari’a tawaye, suka kuma cigaba da yin ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar tare hanya da yin fashi da makami, ko ƙwace dukiyoyin mutane: shi ne a kashe su idan sun kashe, a kuma tsire su idan suka yi kisa, suka kuma ƙwace dukiya, a kuma yanke hannayensu da ƙafafuwansu amma a saɓa tsakani idan sun tare hanya, suka kuma ƙwaci dukiya amma ba su yi kisa ba, a kuma kore su daga garin zuwa wani garin na daban, a kuma tsare su a gidan fursuna idan tsoratar da al’umma suka yi kawai. Wannan uƙubar ƙasƙanci ne da wulaƙanci a gare su a nan rayuwar duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma wadda ita ce azabar wuta) [al- Ma’ida: 33].