Mu’amalar malaman Musulumci da ƙung...

Egypt's Dar Al-Ifta

Mu’amalar malaman Musulumci da ƙungiyar Wahabiyya

Tambaya

Yaya malaman Musulumci suka yi mu’amala da Wahabiyyawa?

Amsa

Malaman Ahus- sunna sun rusa shubuhohin da Wahabiyawa suka kawo tun lokacin samuwar qungiyar har zuwa wannan lokacin namu, wato sun rusa waɗancan shubuhohin da su kaɗai suka keɓanta da su a cikin Ahus-sunna, misali kamar: haramta tawassuli da neman ceto, da nuna rashin karɓar sallar da aka yi a Masallaci mai kabari a ciki, haka nan yanda suka faɗaɗa ma’anar bidi’a tare da sauƙaƙa lamuran kafirta mutane tare da jefawa mutane kalmar shirka cikin sauqi.

Haka nan sun keɓanta da jefa lamuran furu’a na fiqihu a matsayin Usuli na Aƙida, martanin da malamai suka mayar masu ya kasance ne bisa fahimta ta Ahlus- sunna  ta dukkan wasu hanyoyi da suka samu, misali kamar ta hanyar darussa da huɗubobi, ko ta hanyar rubuta maƙalu a jaridu da mujallu, ko kuma cikin wasu rassa na littafan da aka buga, kai har ma ta hanyar ta’alifai da binciken ilimi mai zaman kansa an samar da su, musamman domin yi masu raddi akan shubuhohinsu.

Haka nan a wannan zamanin ana ta amfani da kafofin sadarwa na zamani domin yi masu raddi, kai lamarin ya kai ga yin amfani da wayoyin hannu masu qwaqwalwa domin aikawa da saƙon raddi gare su ta yanda saƙon zai kai ga ɗaukacin mutane masu yawa cikin sauƙi.

Haƙiƙa yin amfani da waɗannan sababbin hanyoyin abu ne da ya dace da zamani, ba dakatar da amfani da wata kafa aka yi ba  wurin yi masu raddi saboda samuwar wata, kamar yanda malamai suka cigaba da yaɗa ilimi ta hanyar da ta dace kamar yanda aka saba tun daga zamani na farko har zuwa na yanzu da ake ciki, duk manufar haka ita ce haɗa  kan Musulmai da rashin rarraba kansu, abun fata shi ne Allah ya tseratar da al’umma daga fitinu da kuma dukkan sharri da abin ƙi.

Share this:

Related Fatwas