Yi wa mutumin da ba a sanshi ba mubaya’a
Tambaya
Shin zai yiwu a yi wa mutumin da ba a san shi ba mubaya’a?
Amsa
Abin da kowa ya sani ne cewa yi wa mutumin da ba a san shi ba mubaya’a abu ne da bai halatta ba, babu ma yanda za a yi a lamunci haka, to ma ta yaya mutane za su miƙa al’amarinsu a hannun mutumin da suka jahilta, ba kuma su san shi ba tun asali, wannan ne kuma abin da ya faru da shugaban ISIS da aka ba a san kowane ne shi ba, mutumin da har mabiyansa ba su san shi ba, ba kuma su san komai game da shi ba; ko domin saboda haka kawai wannan mubaya’ar ta lalace, saboda sun jahilci wanda suka yi wa mubaya’a!.
Lallai yin mubaya’a a Musulunci al’amari ne na shari’a da aka bayar da umurnin yinsa, lallai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi a Bai’atul Aƙba ta farko da ta biyu, da Bai’atur Ridhwan. Mubaya’a ƙulallen alƙawari ne, tana kuma kasancewa ne ta hanyar zaɓin masu faɗa- a- ji da suke jagorantar mutane, ana kuma yinta ne akan yi na yi, bari na bari a cikin abin da ba saɓon Allah ba.
Lallai al’amarin mubaya’a abu ne mai girma, sakamakon irin yanda hakan yake kai wa zuwa ga jagorantar al’amurran bayi, da jagorancin ƙasa, da kuma tunkuɗe mata dukan sharri, da jawo mata dukan maslahohi na duniya da lahira; saboda haka a cikin muhimman sharuɗɗan da dole ne su cika a tare da shugaba, dole ne ya zama ya cika sharaɗin adalci da dukan sharuɗɗansa, su kuma zama sanannu a wurin mutane, ya zamana an san halinsa, an kuma sa kyawon tarihinsa, da ma shi ɗin wane ne shi, kafin a ba shi shugabanci, a miƙa masa ragamar jagoranci, dole ne mutane su yi masa mubaya’a akan sani da basira game da dukan al’amurransa da asalinsa da halayensa da nasabarsa; in ba haka ba mubaya’ar za ta zama an yi ta ne akan jahilci, wannan ne kuma zai ɓata ta tun daga tushe, ta yaya mutane za su yi wa mutumin da ba su sani ba mubaya’a?