Dangantakar ISIS da ƙungiyar Ikhwan...

Egypt's Dar Al-Ifta

Dangantakar ISIS da ƙungiyar Ikhwan ta ‘yan ta’adda

Tambaya

Mene ne dangantakar ISIS da ƙungiyar Ikhwan ta ‘yan ta’adda?

Amsa

Ba wata aba ce ƙungiyar ISIS ba da ta wuce sura ta aikace da ta fito daga tunanin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Ikhwan, dalili kuwa shi ne: ƙa’idar nan ta “Kaɗaitar Alhakimiyya” ɗaya ce daga cikin ƙa’idodjin da ƙungiyar Ikhwan ta ta’addanci ta ginu akansa, wannan abu ne da babu shakka akansa, ma’anarta it ace: rashin yin hukunci da abin da Allah ya saukar kafirici ne da yake fitar da mutum daga Musulunci, wannan kuwa ma’ana ce ta kuskure, babu wani daga cikin jagororin malamai da ake la’akari da su da ya faɗi haka, abin da ake nufi da kafirci a inda Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, to lallai waɗannan su ne kafirai) [al- Ma’ida: 44], shi ne: kafirci ne da ba kafircin da yake fitar da mutum daga Musulunci ba, ko kuma hakan yana nufin wanda ya ƙaryata hukuncin gaba ɗaya ake nufi, kaman yanda Imam Alɗabariy da wasunsa suka bayyana a cikin Tafsiransu, wani ƙarin kuskuren da masu tsattsauran ra’ayi suka aikata kuma shi ne imani da cewa wai dokokin ƙasa sun saɓa da Shari’ar Musulunci, saboda haka ɗaukacin Musulmai ta hukumomi sun kafirta, farkon wanda ya ƙirƙiri wannan ƙa’idar shi ne Abul’a’ala Almaududiy, sannan Sayyidu Ƙutub ya tarjama zuwa harshen Larabci, ya kuma yaɗa shi a cikin wasu daga cikin litattafansa, musamman “al- Zilal”, saboda haka ne ake ɗaukan littafin “al- Zilal” a matsayin ɗaya daga cikin muhimman litattafan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, fara tun daga ƙungiyar Ikhwan zuwa ƙungiyar Takfir wal hijra, da ƙungiyar Aljahad, da Alƙa’ida, har zuwa ISIS.

Share this:

Related Fatwas