Amfani da gashin dabbobi wajen sana...

Egypt's Dar Al-Ifta

Amfani da gashin dabbobi wajen sana’anta abubuwa

Tambaya

Mene ne hukuncin yin amfani da buroshin da aka yi shi da gashin dabbobi?

Amsa

Ya halatta a yi amfani da gashin da aka ciro daga dabba, haka ne ma hukuncin gashin tumaki da na rakuma, kuma wannan ya kunshi dukan wani nau’i na amfani, da suka hada da sana’anta abubuwa da su, saboda maganar Allah Madaukakin Sarki da yake cewa: (Lallai Allah Madaukakin Sarki ne ya sanya kuka zamo kuna da ikon gina hema ta hanyar amfani da fatun dabbobi, da kuke iya zama a ciki, ku kuma iya daukan su a tafiye – tafiyenku.. ya kuma sanya fatan rakuma, da na shanu, da na tumaki da sauransu a matsayin mafaka da kuke iya daukansa a lokacin ya- da- zangonku a wani wuri, da lokacin tashinku daga wurin, ya kuma sanya cewa daga gashin tumaki, da gashin rakuma, da gashin kadduwa ne kuke sana’anta shimfidun da kuke jin dadi da su a wannan duniyar har zuwa lokacin ajalinku) [an- Nahli: 80]

Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas