Abin nufi da ma’abota fadakarwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Abin nufi da ma’abota fadakarwa

Tambaya

Su wane ne ma’abota fadakarwa, shin abin nufi da haka sune malaman Addini?

Amsa

Allah Ta’ala yana cewa : (Ku tambayi ma’abota sani idan kun kasance ba ku sani ba) {An’nahli:43} abin nufi da Ahlul zikr anan shi ne : ma’abota sani da kwarewa a cikin kowani fanni da ilimi, wannan ya kunshi abin da aka gina lafazin da shi ne na bai daya a ma’anar ayar ba wai dalilinta na musamman ba, daukar lafazin a bisa yalwarsa na ma’ana shi ne mafi dacewa matukar wani abu daban ba zai iya kebance shi ba, sai kaga ana tambayarsa akan dukkan lamuran da suka shafi ilimin addini ko lamuran duniya ga ma’abotanta, fayya ce ma’abota sani a wannan ayar na nuna mana haramcin tambayar wanda ba masana kwararru ba.

Share this:

Related Fatwas