Alfarmar jini

Egypt's Dar Al-Ifta

Alfarmar jini

Tambaya

Yaya kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suka dauki mas’alar alfarmar jini ba a bakin komai ba?

Amsa

Lallai kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi sun yi watsi da manufofin shari’ar Allah Ubangiji da Annabawa suka zo da su a cikin litattafan Allah, wanda a cikin wadannan manufofin akwai kiyaye ran dan Adam, da kiyaye alfarmar rai, haka kuma sun fadada wajen kafirta mutane, da warware addininsu da mafi kankantar shubuha da zato, wannan sai ya kai su ga daukan jini ba a bakin komai ba, ga shi nan a cike a cikin tarihinsu na da, da na yanzu, inda suka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, suke kuma tayar da nakiya da bama- bamai a wuraren da suke amintattu ne a ciki, suna kuma yanka su, duk wanda ba ya kan manhajinsu suna kafirta shi, su fitar da shi daga Musulunci su kuma halatta jininsa ba tare da hakki ba, duk kuwa da cewa shari’a ta girmama al’amarin kiyaye rai, da alfarmar jini, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Wanda duk ya kashe rai ba a wurin kisasi ba, ko ya yi barna a bayan kasa, to tamkar ya kashe daukacin mutane ne, wanda kuma ya raya shi shi ma tamkar ya raya daukacin mutane ne) [al- Ma’ida: 32], Ibn Abbas ya ce: duk wanda ya kashe rai guda daya, ya keta alfarmarsa, to daidai yake da wanda ya kashe daukacin mutane, Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai Allah mai girma da daukaka ya haramta maku zubar da jinin junanku, da cin dukiyoyin junanku, da cin mutuncin junanku ba tare da hakki ba) [al- Bukhari], haka ma yana cewa: (Wallahi gushewar duniya ta fi sauki a wurin Allah akan kashe mumini daya ba tare da hakki ba) [Ibn Majah], lallai shari’ar Musulunci mai haske na wani bigire ne, su kuma wadannan mutanen suna wani bigiren na daban.

Share this:

Related Fatwas