Kallon da kungiyoyin ‘yan ta’adda k...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kallon da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke yiwa wasu sashen al’amura na bai daya.

Tambaya

Ta yaya masu tsattsauran ra’ayi suke kallon lamuran masu muhimmanci da suka shafi al’umma, kamar matsalolin mata da wasannin kwaikwayo da dokokin zamani, da dai sauransu na lamurorin da ke damun al’umma?

Amsa

Lallai ma’abota irin wannan karkataccen tunanin suna nunawa mace kiyayya sannan suna haramta mata fita daga gidanta wai sai da lalura, hakanan kuma suka ce karatu da yin aiki ba su daga cikin abubuwan bukata da za su iya sanya mace ta fita daga gidan mijinta, idan har haramtawa mace yin aiki wuce gona da irin ne na bukatarta da zata iya nema a zamanin da take ciki, to lallai haramta mata neman ilimi da fita domin nemansa na zamowa wuce gona da iri ne mai alfanu kuma mai tsanani akan wani abu da take bukatuwa zuwa gareshi a yanayin da take ciki da kuma abin da zai zo mata nan gaba.

Hakanan kamar yanda masu kafirta mutane suke gani cewa ita daular musulunci ita ce wacce take hana waka da kida da wasannin motsa jiki da sauran ayyukan fannoni, sannan wadannan mutane ba su amincewa da bankuna na kasuwanci da kasuwannin hannun jari da kuma tsarin amsa ko bayar da bashi, sannan kuma suna bin wani tsari ne na koyarwa wanda ke dora mutane akan dawowa daga rakiyar wayewar zamani da yanayin rayuwar yau da kullum a duniya, domin komawa bisa tsarin rayuwa irin na magabatan bayi kamar yanda su suka fahimta, wato dai su kasa irin tasu ita ce wacce take haramta daukar hoto da yin dab’i na rubuce rubuce da zane zane haramtawa irn na shari’a, kuma suna haramta yin mu’amala da duk wani abu da yake da danganta  da hotuna da daukar hoton, kamar dai wuraren da na’urorin daukar hoton kamar su kyamara da kayan zane da da talabijin da cinema da dangoginsu.

Hakan irin wadannan mutanen suna ganin cewa daular musulunci ita ce wacce take haramta ayyukan kamfanoni da cibiyoyin ma’aikatu da bankuna da wuraren canjin kudade wacce ake samar da su karkashin dokokin da aka samar a kasa saboda sun sabawa hukuncin Allah, hakanan suna hana mu’amalar kudade domin suna ganinsu a matsayin ayyukan riba ne a cikin kasashen musulmai ko kuma yin mu’amala ne tare da kasashen kafirai, domin kuwa irin haka – karara – ya sabawa koyarwar addinin musulunci.

Share this:

Related Fatwas