Hadisin “An aiko ni da takobi”

Egypt's Dar Al-Ifta

Hadisin “An aiko ni da takobi”

Tambaya

Da yawan masu tsattsauran ra’ayi suna jingina ga Hadisin “An aiko ni da takobi” wurin aikata ta’addancinsu, shin wannan Hadisin sahihi ne? kuma mene ne ma’anarsa?

Amsa

Wannan Hadisin ya zo ta hanyoyi da yawa, malaman Hadisi sun karfafa wannan Hadisin, lafazin “takobi” ya kebanta ne da Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam shi karan kansa ko kuma wanda yake matsayinsa, kuma wannan Hadisin zai iya daukar ma’anar cewa ya zo ne domin kwankwasa kwakwalan wadanda ba musulmai ba ne domin ya tuna musu irin karfin da yake da shi da kuma iko daga Allah.

Wannan Hadisin yana rataye da farlanci na jihadi, yana daga cikin abun da babu shakka a cikinsa shi ne nassosi sun zo da yawa da suke magana akan jihadi, amma duk da haka akwai ka’idoji da yawa akan wannan, kamar dai sauran abubuwa na shari’a, kamar dai yanda lamarin yake a wurin ma’abota ilimi, shi jihadi farali ne na kifaya, Allah Ta’ala ya ce: (Bai kamata ace duk muminai su yi kaura daga wurarensu ba, ina ma da ace wani sashe daga cikin su muminan sun tashi daga wurin domin su fahimci wani abu na addini domin yiwa jama’arsu gargadi da shi idan suka dawo garesu wata kila su wadanda suka zauna din sa wa’azantu) [Tauba:122], yana daga cikin abin da yake sananne anan shi ne musulunci yana matukar kokarin isar da sakonsa zuwa ga duniya, shi jihadi bai kasance ba face hanya ce cikin hanyoyin isar da sakon, abin da yake sahihi anan shi ne umurni da yin jihadi ya takaita ne akan abin da shugaba yake gani shi ne mafi dacewa da musulunci da musulmai na daga yaki ko aminci, amma bai zama dole sai an yake su ba sam sam, ko a tilasta musu yin sulhu, idan aka samu aminci daga wadanda ba musulamai ba ta hanyar shuagaba ko ta waninsa da sharudansa to ya zama dole dukkan musulmai su cika wannan alkawarin, bai halasta a kamasu ba ko daukar wani abu daga garesu ba kamar dukiyarsu face ta hanyar shari’a, kuma bai halasta a sanya musu haraji ba bisa ka’ida ba.

Share this:

Related Fatwas