Bai wa ‘yan ta’adda mafaka
Tambaya
Mene ne hukuncin bai wa ‘yan ta’adda mafaka da bas u maboya, ana riya cewa ana taimakonsu ne akan jahadi saboda Allah?
Amsa
Bai wa ‘yan ta’adda mafak babban laifi da zunubi ne, da wanda duk ya yi Allah Madaukakin Sarki ne zai tsine masa, riya cewa hakan taimakon jihadi ne, wannan tsantsar karya ne aka yi wa shari’ar Musulunci; lallai abin da wadannan mabarnatan suke aikatawa na lalata kayan al’umma da kisa shi ne mafi munin nau’o’in bagayu da barna da Shari’ar Musulunci ta zo domin ta kawar da su, da yakar wadanda suke yi idan ba su daina cutar da ‘yan kasa ba, kiran haka da suna jihadi wannan kuma karya ne da yunkurin yi wa masu karamin tunani rufa- rufa, domin lullube wannan barnar da karyar, dole ne ga dukan al’umma sawa’un daidaikun mutane da kungiyoyi da cibiyoyi su fito su kalubalanci wadannan mabarnatan hawarijawa, da dakile zaluncin da suke yi, kowa gwargwadon matsayinsa da ikonsa; lallai Shari’ar Musulunci ta bayar da umurnin a hana azzalumi yin zaluncin da yake yi, kuma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana yi gargadi akan nuna- halin- ki- in- kula akan zalunci, hasali ma ta sanya hakan cikin laifuffukan da suke jawo fushi da azabar Allah, saboda rashin kula laifi ne da shi yake samar da yanayin aikata laifuffuka ya kuma taimaka wajen yada su, su girma su kagama ba tare da daukan mataki ba; Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai idan mutane suka ga azzalumi ba kuma su hana shi yin zaluncin ba, to kuwa lokaci ya yi da Allah zai yi masu azabarsa duk cikansu) [Ahmad, da Abu Dawud, da al- Tirmiziy, Ibn Majah da Ibn Hibban sun inganta shi, daga cikin Hadisan Abubakar al- Siddik (Allah ya kara yarda da shi)].
Allah shi ne masani.